Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi luguden bama-bamai kan dakarun kai daukin gaggawa na RSF a Khartoum, yayin da kuma a jiya Alhamis sabon fada ya barke a yankin Darfur.
Lamurran sun auku ne bayan da bangarorin masu rikici da juna, suka amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da karin awa 72 bayan karewar na farko.
Yarjejeniyar farko ta tsawon kwanaki uku da aka sha karyawa ta kare ne a daren jiya Alhamis, sai dai gabanin karewar wa’adin ta, shugaban mulkin sojin Sudan Janar Abdul Fattah al Burhan, da kuma babban kwamandan dakarun RSF Muhammed Hamdan Daglo, suka amince a kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta, biyo bayan matsin lamba daga Saudiya da Amurka.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, kungiyar Tarayyar Afirka, Majalisar Dinkin Duniya, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Birtaniya da Amurka sun yaba da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi, da kuma yadda bangarorin sojin masu rikici da juna suka amince da zurfafa tattaunawar sulhu.
Ya zuwa yanzu akalla mutane 512 suka mutu, wasu 4,193 kuma suka jikkata a fadan na Sudan, sai dai jami’an lafiya sun ce yawan mamatann ka iya zarta wanda aka bayyana da adadi mai yawa.
Tuni dai bangaren kiwon lafiya ya ji jiki matuka a kasar, domin kuwa ruwan bama-baman da ya shafi asibitoci ya sa sama da kashi biyu bisa uku ba sa aiki a birnin Khartoum kamar yadda kungiyar likitoci ta tabbatar.
Hukumar samar da abinci ta duniya ta ce kazamin fadan na Sudan na iya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa, domin kuwa a halin yanzu ma alkalumma sun nuna cewar akalla kashi 1 bisa 3 na yawan ‘yan kasar miliyan 15 ke bukatar agaji.