Mutane 10 Sun Kone Kurmus a Wani hari na Tankar Man Fetur

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane goma a wani hatsarin tankar man fetur a mahadar hanyar Bauchi, dake nan cikin garin Jos.

A wata sanarwa daya aikewa manema labarai, kakakin rundunar, DSP Alfred Alabo ya ce gawarwakin mutane goma da suka kone kurmus, an ajiye a mutuware a asibitin kwararru na jihar Filato.

Sanarwar tace motoci uku da keke NAPEP biyu ne suka kone.

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Mutane 10 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Tankar Man Fetur A Jos, Najeriya

Wasu da suka ga yadda hadarin ya auku sun shaida cewa motar dake dankare da man fetur ce ta kwace wa direban ta fadi a kan hanya dake da cinkoson mutane, wanda ya janyo rasa rayuka da jikkatan wadansu mutanen.

Bayan aukuwar hadarin ne matasa suka farma jami’an hukumar kiyaye hadura da ‘yan kwana-kwana da suka zo don yin agaji, bisa cewa basu kawo agaji a kan lokaci ba

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments