A yau Alhamis kakakin ma’aikatar tsaron kasar China Tan Kefei, ya bayyana shirin maaikatar su na ceto yan kasar su da suka makale a kasar Sudan mai fama da rikici
Tun a kwanakin baya, rikici ya kara munana a kasar don haka kasar Sin ta tura jirgin ruwa na soja zuwa kasar domin kwashe Sinawan dake kasar ta Sudan.