Wasu da ake zargin Yan bindigar ne sun bindige jamian tsaro kimani su 20 da suka hada da sojoji 15 da Yan sanda biyar a jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Zuru ta jihar Kebbi kana ya hada da garuruwan Kanya da Danko-Wasaga.
Rahoton ya bayyana cewa sojojin da suka rasa rayukan su sun fito ne daga bataliyar Light Tank ta sojin Najeriya.
A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Allah wadai da irin wadannan ayyukan Yan taadda a jihar ta Kebbi biyon bayanan kashe mayakan sa kai 68 da Yan taaddan suka Yi a jihar ta Kebbi.