Manyan sojojin kasar Nijar da su ka hambarar da gwamnatin farar hula su ka dare kan karagar mulki, a kasar sun yi barazanar halaka Mohamed Bazoum.
Legit ta kawo rahoton cewa a yammacin Jiya Alhamis sojojin da su ka yi juyin mulki sun nuna idan makwabta suka shigo da yaki, za a rasa Mohamed Bazoum gaba daya.
Wani babban jami’in Jamhuriyyar Niger ne ya sanar da karamar Sakatariyar gwamnatin Amurka, Victoria Nuland cewa ba za su yarda da katsalandan ba.
Kamar yadda Nuland ta yi bayani, tace sojan wanda ya na cikin wadanda suka kifar da gwamnati ya yi magana ne ba tare da ya bari an kama sunansa ba.
Bazoum ya na tsare tun ranar 26 ga watan Yuli da aka hambarar da gwamnatinsa.
Kwanaki kadan da sauka daga karagar mulki ta hanyar nuna masa kan bindiga, tsohon shugaban Jamhuriyyar ya yi bayanin irin azabar da yake sha.