Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta shirya tsaf don cika duk wani umarni da shugaba Tinubu zai ba su na yakar kasar Niger.
Babban hafsan Hafsoshin rundunar na kasa, Air Marshall Hassan Bala Abubakar ne ya bayyana hakan a wani babban taro da ya yi da kwamandojin rundunar.
Air Marshal HB Abubakar ya ce rundunar za ta ci gaba da mika wuya da yin biyayya ga shugannin fararen hula a kowane lokaci, sannan za ta ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana.
Babban hafsan Hafsoshin rundunar mayakan saman Kasar, Air Marshall Hassan Bala Abubakar
Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Najeriyar ya yi bayanin cewa yanzu haka abin da ke faruwa a Najeriya da ma makwabtanta a Afirka ta yamma wani sha’ani ne mai sarkakiya da ka iya tasiri kan yanayin siyasar yankin.
Rundunar mayakan saman Najeriya
Wannan dai duka na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ke baiwa dakarun kasashen umarni su zauna cikin shiri don afkawa kasar Nijar da nufin maido da demokradiyya muddin sojojin juyin mulkin suka ci gaba da bijirewa ka’idoji da sharuddan da aka gindaya masu