Kasar Sin ba za ta nemi yi wa kasashen duniya babakere ba
Shugaban kasar China Xi Jinping, ya bayyana cewa kasar sa bata da niyar yiwa wata kasa a Duniya karfa-karfa.
Jinping ya bayyana hakan ne yayin taron kaddamar da mambobin JKS karo na 20 a yau Lahadi
Yace kasarsa ba za ta taba neman yi wa kasashen duniya babakere ko fadada ikon ta a yankunan su ba.
A cewarsa, kasar Sin ta tsaya ne tsayin daka, wajen adawa da duk wani nau’i na babakere da neman iko da yakin cacar baka da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe da kuma nuna fuska biyu