Lamari Ya Dagule Bayan Atiku Yace Arewa Bata Bukatar Bayerabe Ko Ibo Ya Mulki
Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, lamura na kara dagulewa a bangaren dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yayin da bayyana cewa yan arewa basa bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulke su a 2023
Wannan furuci na tsohon mataimakin shugaban kasar ya tunzura mutane da dama, inda suka zarge shi da kada gangar kabilanci
A wani bidiyo da ya yadu, an jiyo Atiku yana cewa shi ya fahimci gaba daya yankunan kasar kuma abun da yan arewa suka fi bukata a yanzu shine wani daga arewa ya shugabance su.