Hukumar hisbah ta jihar kano ta tabbatar da shirin ta na rubanya kokarin da take yi na ganin matasammu sun kaucewa dabi,ar aron bakin dabiun da ba namuba.
Dalilin hakan yasa hukumar ta yi zagaye a fadin birnin kano yayin bukukuwan ranar takutaha domin duba irin tsarin shigar ds matasan sukayi kuma sukayi nasarar kama matasan da sukeyin askin rashin ta ido domin kwalkwale musu kan nasu.
Idan za,a iya tunawa tunda farko hukumar tasha bin wuraren kukukuwan sallah da matattarar matasan domin hanasu aykata ba dai dai ba da kuma da kile aronbakin dabi,u kamar yaddata samu ayau asabar yayin bikin ranar takutaha.
Majiyarmu ta jiyo mana cewa sashen yada labarai na hukumar ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya domin hana ayyukan badala da matasan kan fake da wani al,amari na farin ciki su baje hajarsu ta rashin ta ido.
Tun da farko sun bayyana cewa umarnin Babban kwamandan hukumar ne na a dakile ayyukan rashin tarbiyya a tsakanin matasa maza da mata.
Hukumar ta kuma sa ido a dangane da dauke dauken hotunan matasa maza da mata sannan ta hana mata zama a gefen babur mai kafa uku tare da daidaita sahun maza da mata a yayin bikin takutahar