Shawarar gwamnonin APC ga Tinibu ta jawo cece-kuce a Majalisa

Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya sun soki yadda Gwamnonin jihohi suka bada shawarar ayi kason mukaman da ake da su.

Rahoton Premium Times ya bayyana shawarar Gwamnonin APC a karkashin kungiyar PGF ba ta samu shiga ba, ‘Yan PDP da APC sun soki matsayar.

Honarabul Akin Alabi na jam’iyar APC, daga jihar Oyo ya yi watsi da wadannan shawarwari da aka ba wa Bola Tinubu a matsayinsa na zababben shugaban kasa.

Alabi ya nuna zai yi wahala jam’iyyar APC ta ware manyan kujerun majalisa ga yankin Arewa, la’akari da tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments