Yayin da ake tururuwa zuwa aikin Umrah, hukumomin Saudiyya sun gargadi masu ziyara a wannan shekarar, rahoton BBC.
Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta bayyana cewa, akwai bukatar jama’a su ke daraja wuraren ibada masu alfarma a ziyarce-ziyarcensu.
Wannan na zuwa ne tare da bayyana bukatar a bi dokokin da hukumar ta gindaya wajen takaita daukar hotuna a masallatan Haramin guda biyu.
A cewarta, abu ne mai muni a ga tarin Musulmi sun shagala da daukar hotuna a madadin mai da hankali kan yin ibadar da ta kawo su kasa mai tsarki.
bangare guda, hukumar ta bayyana gargadi kan jama’a da su guji hadawa da wasu mutanen da babu ruwansu a cikin hotunansu ba tare da izini ba.
Wannan na nufin, an hana jama’a daukar hotuna a wurare masu cunkoson jama’a, inda hukumar tace hakan na kara yawan cunkoso a masallatan, rahoton Saudi Gazette.