Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi karin haske game da eNaira da ya kaddamar, inda yace an yi sa ne don takaita kashe tsabar kudi da kuma rungumar hada-hadar kudi ta yanar gizo. Samuel Giwa,
Mukaddashin manajan CBN na Akure ne ya ba da wannan bayanin a lokacin da ya ziyarci fadar Deji na lardin Akure, Oba Aladetoyinbo Adedelusi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Giwa ya ziyarci fadar ne domin neman goyon bayan jama’ar Ondo wajen amfani da manhajar eNaira a hada-hadarsu ta yau da kullum.
Da yake jawabi ga jama’a, Giwa ya ce, eNaira zai habaka wa ‘yan Najeriya hanyoyin musayar kudade, zai rage rashawa da damfara kana ya kara fadada harkar hada-hadar kudi ga ‘yan kasar.
Ya kara da cewa, eNaira ba wai kudi bane kawai ba, wata hanya ce ta kirkirar damammaki na musayar kudi da kuma saukaka hanyoyin hada-hada ga ‘yan kasar cikin sauki da tsaro.
A cewarsa: “Babu shakka tsarin eNaira ya zama wani muhimmin ginshiki na tsarin hada-hadar kudi a Najeriya da kuma samar da wata hanya ta daban wajen hada-hada.