Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da ranar 15 ga watan aprilu a matsayin ranar da zata gudanar da zaben gwamnoni da yan Majalisun jihohi da bai kammala ba
INEC ta sanar da hakan ne ta bakin sakataren yada labarai na hukumar Rotimi Oyekanmi a yau Litinin
Oyekanmi yace hukumar ta cimma hakan na bayan taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a yau Litinin