Dalilan ganawar Tanko Yakasai, Bisi Akande da Tinibu

Dattawan ƙasa, Alhaji Tanko Yakasai da Chief Bisi Akande, sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Manyan jiga-jigan sun yaba da kamun ludayin sabon shugaban ƙasan, inda aka ji suna cewa ‘yan Najeriya na cikin farin ciki a yanzu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Dattawan biyu, waɗanda ake wa kallon abokanan Tinubu ne a siyasa, sun bayyana haka ne yayin zantawar su da yan jaridan gidan gwamnati a Abuja bayan ganawa da Tinubu.

Yakasai da Akande sun ce shugaban kasa Tinubu zai nuna wa duniya banbancinsa da sauran shugabannin da aka taɓa yi a baya a ƙasar nan.

Da yake jawabi, Alhaji Tanko Yakasai, ya tuna lokacin da Tinubu ya kai masa ziyara kuma ya nemi shawarinsa da albarka gabanin ayyana kudirin neman takarar shugaban ƙasa.

A cewarsa, bisa la’akari da haka, yanzu lokaci ne da ya kamata ya ziyarce shi domin taya murna da kuma tabbatar masa da goyon baya, The Cable ta tattaro.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments