Attajiri dan kasar Faransa, Bernard Arnault ya ga yadda dukiyarsa ta tashi zuwa sama da $200bn a rana daya, inda ya bar Elon Musk a baya
Karin kudin Arnault na zuwa ne a daidai lokacin da kamfaninsa na kayan karau, LVMH ya samu cinikin $12bn a lokaci guda
A bangare guda, a nan gida Najeriya, Aliko Dangote ya samu karuwar sama da $538m a rana guda daga kasuwancinsa
Attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Bernard Arnault na ci gaba da yiwa Elon Musk fintinkau a cikin wannan shekarar.
A cewar rahoton Bloomberg, attajirin dan kasar Faransa ya yi cinikin kayayyakinsa na karau, inda Tesla, kamfanin Elon Musk ke ja da baya.
Arnault ya kafa tarihi a fannin karin dukiya Bloomberg ta ce, Arnault ya samu karin $12bn a dukiyarsa a ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu, inda kudinsa yanzu ya kai $210 da ba a taba samu ba a rana daya.