Hukumar zabe ta fara rarraba kayan zabe a jihar Adamawa

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Adamawa ta fara rabon kayayyakin zaɓe a wuraren da za a gudanar da zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar a ranar Asabar.

Hukumar ta INEC ta bayyana zaɓen gwamnan jihar na watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, domin yawan katin zaɓen da aka karɓa a wuraren da aka soke zaɓen ya zarce tazarar da aka bayar a zaɓen.

Fafatawar dai ta fi zafi ne a tsakanin Sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar mai ci yanzu, Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya ke kan gaba da ƙuri’u 30,000.

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinonin zaɓen biyu hukumar INEC na ƙasa, Farfesa Abdullahi Abdulzuru da Dr. Baba Bola, suna wajen domin sanya ido kan yadda rabon kayayyakin zaɓen yake gudana a ranar Juma’a.

Da yake tattaunawa da ƴan jarida, kwamishinan zaɓen INEC na jihar, Barr. Hudu Ari, ya ce hukumar ta shirya tsaf sannan tana fatan zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Dukkanin kayayyakin aikin zaɓen an raba su. Za su isa zuwa wuraren da ake buƙatar su cikin lokaci.” A cewar sa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments