Daga Walid Hari.
Wani bidiyo da ke jan hankula a shafukan sada zumunta wanda ke nuna wasu ‘yan makarantar firamare aji na biyu na datse kan wata kaza ya tayar da hankula kan sabuwar manhajar karatu ta kasar Kenya.
Sabuwar manhajar na son dalibai su fi mayar da hankulansu kan ainihin aiwatar da abubuwan da ake koyar da su maimakon tsabar karatu kawai.
Wannan bidiyon ya ja hankulan jama’a, inda yawancinsu ke bayyana damuwarsu ga kiyaye lafiyar yaran.
Tun da suka fara karatu a makarantar firamare daliban sun kasance abin gwaji kan sabuwar manhajar karatu ta kasar.
Wasu iyayen da ba za su iya biyan kudaden da ake karba a hannunsu akai-akai ba sun gwammace mayar da ‘ya’yansu makarantu masu zaman kansu.
Wasu malaman kuma na ganin gwmnati ce ya kamata ta rika ba makarantu tallafi kayayyakin gudanar da darussa, sai dai ko za ta hada da kaji wani abu ne na daban.