Dangote yayi Karin Haske dangane da yadda ya mallaki kamfanin Ciment na Obajana

Shugaban rukunin kamfanin Dangote Industries Limited ya bayyana cewa an bi dokoki da matakan da suka dace wajen sayen filin kamfanin simintin Obajana a shekarar 2002.

Jaridar This Day ta ruwaito Dangote na bayyana sabanin abin da gwamnatin jihar Kogi, take ikrari na cewa an mallaki kamfanin ne ba tare da an bi ka’ida da doka ba.

Bugu da kari Dangote, yace yana biyan gwamnatin Kogi haraji da duk wasu kudi da suka kamata tun lokacin da suka fara aiki a 2007.

Dangote da Yahaya Bello Sun Gurfana a Fadar shugaba Buhari domin Yi Musu sulhu kamar yadda kamfanin ya fitar a jawabin sa na karin Haske da yayi ga manema labarai.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments