Karbar na goro a hannun direbobin manyan mota a Najeriya ya zame mana masifa’
Daga Walid Hari.
Wani matuƙin babbar motar dakon kaya a Najeriya ya koka kan yadda cin hanci yake yin mummunan tasiri a kan aikinsa da yake yi na jigila tsakanin arewa da kudancin ƙasar.
Mutumin ya ce baya ga barazanar tsaro da suke cin karo da ita a kan hanyoyin da suke bi ɗin, ya yi zargin cewa jami’an tsaro kuma kan dinga tatike su da karɓar na goro ba tare kuma da sun samar musu wata kariya daga komai ba.
Bello direba yace “Sau da dama idan na tashi daga Sakkwato zuwa Fatakwal wallahi duk checkpoint din da na zo sai sojoji sun karɓi a ƙalla naira 5,000 ko fiye da haka.”
Bello ya ce yakan bi hanyoyin Fatakwal da Enugu da Aba daga ko dai Kano ko Sakkwato kusan sau uku a duk wata ɗaya.
Direban ya kuma koka kan yadda a ƙoƙarin karɓar na goron nan da jami’an ke yi yake jawo cunkoson ababen hawa a kan hanyoyin inda ake sa su ɓata lokaci sosai.
“Ga hada go slow da suke yi ga kuma cin zarafin duk wanda bai ba su kudin ba”.