An kama wani ɗan jaridan Amurka da ke aiki da jaridar Wall Street Journal a Rasha inda aka zarge shi da ayyukan leƙen asiri.
Evan Gershkovich, wani gogaggen mai aika rahotanni ne a Rasha, kuma yana aiki a birnin Yekaterinburg lokacin da aka kama shi aka tsare.
Jaridar The Wall Street Journal ta ce tana cikin “matsananciyar damuwa” game da tsaron lafiyarsa kuma da kakkausar murya ta musanta zarge-zargen da aka yi masa.
Fadar Kremlin ta shugaban Rasha ta yi iƙirarin cewa an kama ɗan rahoton ne “dumu-dumu da laifi”.
Hukumar ayyukan leƙen asirin Rasha ta FSB ta ce ta “dakatar da haramtattun ayyukan” ɗan jaridan wanda ta ce ya riƙa “aiki bisa umarnin Amurka” kuma ya “tattara sirrukan ƙasar”.