Gwamnatin tarayya na shirin fara rabon hatsi da takin zamani da kuma karin albashin ma’aikatan gwamnati, daga ranar Litinin mai zuwa a cewar ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne don dakile tasirin tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar ga al’ummar kasar nan.
Sanarwar da ofishin mataimakin shugaban kasa ya fitar ta ce za’a raba hatsi da taki ta babban bankin tarayya CBN, kuma gwamnonin jihohi sun goyi bayan shirin. Sai dai bayar ta ba da cikakken bayani kan matakan rabon ba.
A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu na ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya don taimakawa wajen magance wahalhalu da tashin farashin man fetur ya haifar bayan dakatar da tallafin man fetur a watan Mayu.