Duk da fadakarwa da magabata suka yi wa ‘yan siyasa har yanzu ana samun kalamai da ka iya tunzura jama’a da tayar da fitina a lokutan zabubbuka.
To sai dai rundunar ‘yan sanda ta kasa ta ce tana nazarin kalaman da ‘yan siyasa ke yi masu tayar da husuma kuma zata yi dirar mikiya kan wadanda ta samu da hannu ga munanan kalaman.
Yadda aka gudanar da zabubukan shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin tarayya, baya rasa nasaba da abin da ke ci gaba da tunzura wasu ‘yan siyasa suna furta kalamai munana wadanda ke iya tayar da fitina a zaben da ke tafe na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Alalmisali irin yadda rundunar ‘yan sanda ta ayyana neman dan majalisar dokoki na mazabar cikin garin Bauchi, ruwa a jallo, akan zargin hada baki da tayar da fitina, manuniya ce ga yadda ‘yan siyasa ke rura wutar fitina duk da hannunka mai sanda da ake yi musu.