Kungiyar tabbatar da daidaito da adalci a ma’aikatun gwamnati ta SERAP ta bukaci shugaban kasar Amurka Joe Biden yayi amfani da karfin ikon da yake da shi ya dakatar da bayar da visar shiga kasar ga shuwagabanni da yan siyasa da masu rike da madafun iko masu tada hatsaniya a lokacin zabe a Najeriya.
Kungiyar ta nemi dakatar da bayar da visar ne a wata was da ta rabawa manema labarai bayan samun rahoton rikita-rikitar zabe da ta faru a wasu jihohin kasar nan
Jihohin da abin ya shafa sun hadar da Akwa Ibom, da Enugu, da Gombe, da Lagos, da Edo, da Ogun, da Osun, da Rivers, da kuma Taraba