Rahotanni na nuni da cewa kimanin mutane 150 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu ciki har da tarin kananan yara bayan share tsawon kwanaki biyu ana bata-kashi tsakanin Hausawa da kabilun da ke rayuwa a yankin kudancin jihar Blue Nile na kasar Sudan.
Rikicin wanda ya samo asali daga batun mallakar filayen noma da kiwo, an ittifakin shi ne Rikici mafi muni da aka fuskanta a baya-bayan nan tsakanin kabilun da ke zama a yankin kudancin jihar Blue Nile.
An kwashe kwanaki biyu ana gwabza fada mai muni tsakanin kabilun a yankin Wad al-Mahi mai tazarar kilomita 500 da birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda shugaban yankin Abbas Moussa mabanbantan kabilun sun farwa juna lamarin da ya kai ga jikkatar mutane akalla 86 baya ga dimbin rayukan fiye 150 da suka salwanta galibi Mata da yara da kuma tsofaffi.
Tuni dai al’ummar yankin suka fara wata zanga-zangar bukatar kawo karshen rikicin tare da kira ga gwamnatin kasar kan ta sauke gwamnan jihar wanda suke zargi da assasa rikicin.
Masu zanga-zangar rike da allunan bukatar sauke gwamnan sun rika rera waken cewa basa bukatar tashin hankali da rikici.
Shirin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi gargadin yiwuwar fuskantar tashe-tashen hankula a yankin na Blue Nile sakamakon yadda makamai ke bazuwa a yankin wadanda ake shigar da su daga Habasha da kuma Sudan ta kudu dukkaninsu masu fama da yake-yake.
Babban jami’in Majalisar a Sudan Eddie Rowe ya ce tun farowar rikicin a ranar 13 ga watan Oktoba akalla mutane 170 suka mutu yayinda wasu 327 suka samu munanan raunuka tsakanin kabilun biyu.