Rikicin kabilanci ya jawo asarar rayuka sama da 200 a Sudan

Jami’ai a Sudan sun ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin ƙabilanci da ake yi a kudancin kasar tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Berta ya ƙaru zuwa 200.

Wani shugaban al’umma a Jihar Blue Nile ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyuwa uku, inda ya yi kira ga kungiyoyin agaji da su taimaka wajen binne gawarwakin wadanda suka rasu.

Rahotanni na cewa ana rikici tsakanin Hausawa da Berta ya ɓarke ne kan gonaki.

A jiya Juma’a aka sanya dokar ta-ɓaci ta tsawon kwana 30 a fadin jihar ta Blue Nile.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments