Allah ya yiwa tsohon Wazirin Kano kuma babban limamin masallacin Juma’a na Fagge rasuwa a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni
Sheikh Nasir Muhammad Nasir wanda aka fi sani da limamin Waje ya rasu ne yana da shekara 87 a duniya bayan ya yi rashin lafiya
Babban limamin an taɓa naɗa shi sarautar Wazirin Kano, kafin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya cire shi