Daga Hassan Umar Gwammaja
Haihuwa, ita baiwace da Allah (SWA) Yake baiwa wanda yake so ya kuma hana wanda yake so, amma a bangarin mata iyayanmu wajan haihuwar ‘ya’ya da Allah kan basu wasu yakan zo musu da Jarrabawa, wasu na larura wasu har takai su ga rasa ransu dungurungun
Kamar yarda wata mata ta hadu da nata ajalin a sanadiyar haihuwar ‘yan 3
Ita dai wannan mata mai suna Hassana ta rasu bayan ta haifi ya’ya nata guda uku.
A cewar kakar yaran tun bayan rasuwar mahaifiyar su aka damka su a hannun kanwar mahaifiyar su inda ta cigaba da rainon su
Kanwar mahaifiyar tasu mai suna Husaina tace a yanzu haka yaran na cikin bukatar tallafin madara da kayan saka wa