Yadda Ganawar gwamnoni da shugaban kasa ta jawo cece-kuce

Daga khadija Salisu Danmaliki

Gwamnonin jihohin kasar sun nuna goyon bayansu ga matakin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur.

Gwamnonin sun bayyana haka ne a lokacin wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar a ranar Laraba.

Wata sanarwa da ta fito ta hannun daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban, Abiodun Oladunjoye, ta ce gwamnonin sun rinƙa yin jawabi ɗaya bayan ɗaya a lokacin ganawar, inda suka rinƙa yaba wa shugaban ƙasar kan matakin da ya ɗauka.

Gwamnonin waɗanda suka je fadar bisa jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq sun ce za su yi aiki tare da shugaban ƙasar wajen ganin an magance matsalolin da cire tallafin zai haifar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments