Har yanzu a iya cewa tsugune bata kare ba inda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan kasar nan, yayin da jama’a ke ci gaba da zaman Dar-dar a wasu jihohin
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da a jihar Sakkwato ‘yan bindiga suka hallaka mutane fiye 11; suka kuma yi garkuwa da wasu fiye da dari daya cikin kwanaki uku kacal.
Wasu barayin mutane sun hadu da ajalin su a hannun jami’an yan sanda
Zamu yi iya kokarin mu na magance magudin zabe : INEC
Dankari, Sheikh Ahmad Gumi ya ‘Debo ta gaba daya
Tabbacin kare rayuka da mahukunta ke bai wa ‘yan kasa alamu na nuna shifcin gizo ne kawai domin har yanzu jama’a na zaman fargaba, saboda yanayin da suka tsinci kansu ciki na rashin tsaro a wasu wuraren.
‘Yan bindiga sun kai hari a wani kauye da ake kira Dan Gari dake kusa da garin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sakkwato, a ranar Litinin ta wannan mako da rana tsaka.
Dan Majalisar Dokoki na jiha mai wakiltar yankin, Aminu Almustapha Boza, yace a lokacin maharan sun hallaka mutane 11 a garuruwa 3 kuma kullum sai sun kai hari sun kashe mutane ko sun yi garkuwa da su.
A karamar hukumar Gotonyo mai makwabtaka da Sabon Birni bayanai sun nuna cewa a cikin dare daya na ranar Litinin ‘yan bindiga sun sace mutane kimanin 60 a garuruwa daban daban na karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar Abdulwahab Yahaya Goronyo ya bayyana cewa yana wuya a iya tantance adadin mutanen da ake garkuwa da su a yankin domin kullum sai an kai hari a garuruwa daban daban, ya bukaci jama’a da su dage da addu’o’in samun daukin Ubangiji