Zamu yi iya kokarin mu na magance magudin zabe : INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ba za ta bari a yi maguɗin zaɓe a babban zabe mai zuwa na 2023 ba domin daman ba halinta ba ne.

Sabuwar Kwamishinar Zaɓe ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi ce ta bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula, CSOs.

A cewarta, maguɗin zaɓe zai yi matukar wahala domin hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da sahihin zabe.

Misis Ugochi ta ce: “INEC ba za ta taba yin magudin zabe ba. Ƴan siyasa ne ke tafka magudin zaɓe. Za mu yi iya gwargwadon abin da za mu iya wajen daƙile maguɗin zaɓe.

“Tsarin yanzu ya sanya maguɗin zaɓe ya na da matukar wahala. Idan kuna son yin magudi a yanzu muna da BVAS. Shin ta hanyar satar hanya ta BVAS ne ko kuma kulle rumbun ajiye bayanai inda komai ya ke?

“Yanzu yana da wahala sosai. Wannan lokaci ne da kafafen yada labarai da CSOs za su yi aiki tukuru da kuma wayar da kan jama’a. Mu ba ma nuƙu-nuƙu za mu yi iya kokarinmu a duk abin da muke yi.

“Za mu tsaya tsayin daka domin tare duk wani hari daga waje. Ya kamata kafafen yada labarai su ba mu goyon baya don kada mu samu matsaloli a abin da muka sa a gaba,” inji ta.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments