Rundunar ’yan sandan ta kasa reshen jihar Delta dake ta sanar da kashe wasu mutane biyu da ake zargin masu satar mutane ne yayin wani samame da ta yi a baya-bayan nan
Kakakin ’yan sandan jihar, Bright Edafe, ya shaidawa manema labarai a birnin Warri cewa, an kashe wadanda ake zargin ne a ranar Lahadi yayin da suke kokarin tserewa
A cewarsa, wani ayarin jami’an sintiri ne ya kama wadanda ake zargin a ranar Asabar a Warri, bayan an gano kwanson harsasai 3 a cikin babur mai kafa 3 da mutanen suka yi amfani da shi. Yana mai cewa bayan tambayoyin da aka yi musu, an gano cewa suna cikin wata kungiyar mutane 5 dake satar mutane a yankin.
A ranar Lahadi ne, wadanda ake zargin suka jagoranci ’yan sanda zuwa maboyarsu dake yankin, inda aka gano bindigogi biyu da adduna biyu.
Kakakin ya kara da cewa, a kan hanyarsu ta komawa ofishin ’yan sanda ne suka yi tsalle daga motar ’yan sanda domin tserewa, amma sai ’yan sanda suka yi musu mummunan raunin da ya kai ga mutuwarsu yayin da ake kai su asibiti.