Masana harkokin tsaro a kasar nan suna ganin cewa akwai babbar barazana idan har ‘yan kungiyar Boko Haram da suka mika wuya suka rasa matsugunni daga gwamnatin tarayya.
Masanan sun yi tsokacin ne bayan da hukumomi a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar nan, suka ce ana fama da karancin wurin ajiye dubban ‘yan kungiyar ta Boko Haram da suka mika wuya.
Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi ne kan lamurran tsaro, ya shaida wa manema labarai cewa akwai hadarin gaske idan har gwamnati ko hukumomin tsaro suka gaza wajen samar da matsugunnai ga wadannan ‘yan Boko Haram din.
“Babban hadarin shi ne za su iya kubucewa su koma in da suka fito wato kungiyarsu, saboda da yawa daga cikinsu yunwa ko rashin yarda da wani abu a kungiyar ne ya sa suke fita daga kungiyar su mika wuya.”
Masanin tsaron ya ce idan har suka je sansanin suka ga babu abincin da za a ci a koshi sannan rayuwa ta ki dadi a wajen, ko kuma duk da sun mika wuya an ki yi musu abin da ya dace misali na rashin mayar da su cikin al’umma, to babban abin da za su fara yi shi ne su gudu su koma kungiyarsu.