An sake zaben shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, a matsayin shugaban jam’iyyar ANC mai mulkin kasar.
An gudanar da zaben a jiya yayin babban taron jam’iyyar karo na 55.
Ramaphosa ya kayar da abokin takararsa Zweli Mkhize da kuri’u 2,476 Zweli Mkhize, yayin da Mkhize ya samu kuri’u 1,897.