Masu nazari da suka fito daga jami’ar Queensland sun fito da wani tsarin hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da jarirai ka iya fuskanta tun daga matakin yarinta. Sun gabatar da sakamakon nazarinsu a mujallar ilmin cututtukan kananan yara da lafiyarsu, wadda aka wallafa a Australiya a kwanan nan.
Masanan sunce, sun yi nazarin ne kan sauye-sauyen nauyin jikin jarirai cikin shekara daya bayan haihuwarsu, da yanayin da suke barci, kuma abin nada nasaba da nauyin jikin iyayensu mata da tsayinsu kafin su samu ciki, nauyin jikin iyayensu maza da tsayinsu, ko an haife su kafin lokacin da aka tsara, ko iyayensu mata sun sha taba yayin da suke da ciki, da dai sauransu.
Sakamakon wanda ya yi hasashen barazanar gamuwa da matsalar Kiba, yace jarirai ka iya fuskanta yayin daga shekaru takwas zuwa shekaru tara bayan haihuwa.
Rahoton nazarin ya nuna cewa, an tabbatar da ingancin wannan tsari, bisa bayanan da aka tattara a baya dangane da lafiyar kananan yara kusan dubu 2 a jihar yammacin Australiya daga haihuwarsu zuwa shekarunsu su kai 9 a duniya. Ingancin hasashen da tsarin yake iya yi ya kai kaso 74.6.
Dangane da wannan tsarin hasashen barazanar gamuwa da matsalar kiba da kananan yara ka iya fuskanta, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, bambanta jarirai wadanda suke fuskantar babbar barazanar samun kiba a lokacin yarantaka, yana taimakawa iyalansu daukar matakan yin rigakafi masu dacewa tun da wuri. Bayan da kananan yaran suka zama baligai, mai yiwuwa matsalar kiba za ta ci gaba da addabarsu.
Masana harkar lafiya a kasar Australiya sun bayana cewa, za su ci gaba da tababtar da ingancin tsarin a nan gaba. Idan bukatar hakan ta taso kuma za a fara aiki da tsarin cikin hanzari, a kokarin taimakawa kare kananan yara gamuwa da matsalar kiba.