Shekaru 62 kenan yau da samun yancin kan Nigeria daga hannun turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a wani rubutu da binciken da Aksam media tayi shin wanne cigaba kasar ta Nigeria ta samu a wadannan shekaru?
Daga Walid Y Hari.
Sai dai fa har yanzu kasar na nan na fama bisa kasa kaiwa ga matakin da ake mafarkin zatakai na cigaba ta fannoni da dama na rayuwa a tsawon wadannan shekekaru da aka kwashe.
Fannin ilimi dukda irin cigaba da samar da makarantu tun daga matakin farko na furamare zuwa jami’oi, fannin na cikin wani yanayi mara dadi, akance an samar da makarantu da ajujuwan dalibai wasu kuma an zamanantar dasu to amma ya batun baiwa dalibai madarar ilimin? Baya ga ciyar da daliban makarantun furamare su jami’oi suna aiki kamar sauran na kasashen waje koko anata zaman yajin aikin sai baba ta ganine?
To shikuma fannin tsarofa wai kuwa talakawa na iya tafiya mai dogon zango domin yin fatauci a fadin sassan kasar nan cikin kwanciyar hankali kokuwa yan fashin daji,yan bindiga da masu garkuwa na nanne?