Kwamatin NWC na jam’iyar PDP yayi Bayanin yadda ya karbi makudan miliyoyi na cinhanci.

Dambarwar da ke ci gaba da faruwa a jam’iyyar PDP na sake daukar sabon Salo, inda lamarin ke kara Rikicewa.

Wani rahoto yace, jam’iyyar PDP ta tura wa wasu jiga-jiganta kuma mambobin kwamitin ayyuka na NWC kudi don siye bakinsu Sai dai, jam’iyyar ta PDP ta fito ta yi bayanin kudaden da ta tura, da kuma dalilan da Yasa ta tura su ga wadannan jiga-jigai

Kazalika ta amince da cewa ta tura Miliyon I kudade zuwa asusun bankunan mambobin kwamitinta na ayyuka (NWC), amma ta musanta yin hakan a matsayin cin hanci.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, martanin na PDP na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran jam’iyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar.

Rahoton ya ce, sanarwar da PDP ta fitar martani ne ga kalaman wasu mambobi da ke cewa sun mayar da N20m da aka basu tare da alanta cin hanci aka basu don zama kan wata magana.

Rahotanni a baya sun ce, wasu mambobin NWC hudu sun karbi wadannan kudade, amma daga baya suka bayan da rahotanni suka yayata jita-jitar PDP ta ba mambobin cin hanci ne.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments