Daga Walid Hari
A shekarar 1960 ne Najeriya ta samu ‘yancin nata daga Birtaniya. Sai dai da dama daga cikin matasan kasar na cewa ‘ba su gani a kasa ba’ kasancewar babu wani abu na inganta rayuwarsu da ke faruwa a kasar mai yawan jama’a miliyan 218 a ganinsu.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke tunkarar babban zaben da za a yi a shekara mai zuwa, 2023.
Tun bayan samun ‘yancin kasar, Najeriya ta yi shugabanni 11, inda shida daga ciki suka kasance sojoji sannan biyar farar hula.
Najeriya ce kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka amma wadda kuma wasu ke yi wa kallon tana daya daga cikin mafiya koma-baya a nahiyar bisa la’akari da arzikin da Allah ya huwace mata.
Matsalar rashawa da cin hanci ne dai babban kalubalen da kasar ke fuskanta, al’amarin da ya haifar da kusan dukkkannin matsalolin da ‘yan kasar ke fama da su.