Daga khadija Salisu Danmaliki
Yau ne, ake bikin Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake tunawa da ita a duk ranar, 26 ga watan Agusta.
Akan hakan BBC hausa ta zanta da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, shahararren malami a Jami’ar Usman ÆŠanfodiyo.
Malamin dai ya yi jawabi ne a kan muhimmancin ranar, da al’adu da asalin al’ummar Hausawa, har ma da Æ™alubalen rayuwarsu.
Hausawa dai na cikin al’ummomin da suka cuÉ—anya sosai da sauran Æ™abilun masu maÆ™wabtaka ko hulÉ—ar arziÆ™i da su a cikin Æ™asashen Afirka ta Yamma da É—aukacin nahiyar Afrika, har ma da duniya gaba É—aya.
Ƙiyasi na baya-baya da aka yi cikin shekarun da suka wuce, a cewar Farfesa Muhammad Bunza, ya nuna Hausawa sun kai miliyan 150. Amma dai masana na ganin cewa haƙiƙanin yawan Hausa ya yi matuƙar zarce haka.
Masanan harshen Hausa kamar Bunza sun ce akwai ɗumbin Hausawa a ƙasashe masu nisa da Ƙasar Hausa, kamar Saudiyya da Sudan da Moroko.
Kuma saboda yawan auratayya da kuma kasancewar Hausa, harshen da ke haÉ—a hulÉ—ar ciniki da sauran mu’amalolin rayuwa ga mabambantan Æ™abilu, a wasu lokuta har akan yi tababa shin ko akwai Bahaushen asali ma kuwa?
A gefe guda kuwa yaren Hausa ana amfani da da shi a kasashe kamar su Benin, Burkina Faso, Cameroon, Central African Republic, Chad, Congo, Eritrea, Germany, Ghana, Niger, Sudan, da Togo.
A yanzu kuma a iya cewa guraren da a ka fi amfani da harshen hausa sune Arewacin Nageriya da kasar Niger da Arewacin Cameron da kuma kasar Ghana
Matasan harshen Hausa a Duniya
1 Mandarin: 1090
2 English: 983
3 Hindustani: 544
4 Spanish: 527
5 Arabic: 422
6 Malay: 281
7 Russia: 267
8 Bengali: 261
9 Portuguese: 229
10 French: 229
11 Hausa: 150
12 Punjabi: 148
13 German: 129
14 Japanese: 129
15 Persian: 121
16 Swahili: 107
17 Telugu: 92
Kalubalen da harshen yake fiskantar
Har yanzu duk da yawan al’ummar da suke amfani da harshen hausa wajen magana da mu’amalar cinikayya wanda a Kiyashi suka zarce mutane miliyan 150Â amma babu wani ilimi da ake bayar da shi a dokance da harshen Hausa