Duk da cewa shugaba Vladimir Putin ya yi jawabi ga taron ƙungiyar Brics, amma bai ce uffan ba a kan haɗarin jirgin sama da ake tunanin ya yi sanadin mutuwar shugaban ƙungiyar Wagner, Yevgeny Prigozhin.
Ana kyautata zaton cewa Prigozhin ya mutu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a ranar Laraba, tare da ƙarin mutum tara.
Tun da farko, wani zauren dandalin Telegram mai suna Grey Zone ya ba da rahoton cewa an harbo jirgin ne da wasu makaman kakkaɓo jiragen sama a yankin Tver, na arewacin birnin Moscow.
Jirgin saman, wanda ya tashi daga Moscow zuwa birnin St Petersburgh, ɗauke da fasinjoji guda bakwai da ma’aikatan jirgi uku.
Prigozhin ya jagoranci wani boren sojoji da bai yi nasara a kan rundunar sojin Rasha a watan Yuni.
Shafin Telegram na Grey Zone ya ruwaito mazauna yankin na cewa sun ji ƙarar fashewar wani abu har guda biyu kafin faɗuwar jirgin, kuma sun ga tururi guda biyu a lokacin.
Kamfanin dillancin labarai na Tass ya ce jirgin saman ya kama da wuta a lokacin da ya dira a ƙasa, inda ya ƙara da cewa tuni aka gano gawawwakin mutum huɗu.
Ya ce jirgin ya yi tafiyar ƙasa da rabin sa’a bayan tashinsa.
Kamfanin dillancin labarai na Rasha Interfax ya ruwaito ma’aikatar ba da agajin gaggawa na cewa ana kyautata zaton dukkan mutanen da ke cikin jirgin saman sun mutu, lokacin da ya faɗo ƙasa.