Hukumomin a kasar Faransa sun ce gwamnatin mulkin sojan Nijar ba ta da hurumin korar jakadanta a kasar Sylvain Itte,
Jaridar France 24 ta ruwaito. Sojojin Nijar a ranar Juma’a sun ba ltte sa’o’i 48 ya fice daga jamhuriyar saboda kin amsa gayyatar da aka yi masa na ganawa da ministan harkokin waje da gwamnatin mulkin soji ta nada.
A cewar Ma’aikatar harkokin wajen kasar matakin da gwamnatin Faransa ta dauka ya saba wa muradun Nijar.
Sai dai Faransa ta ce sojojin na Nijar ba su da hurumin korar jakadanta a Yamai, kamar yadda kafar yada labarai ta Deutsche Welle ta ruwaito.
A cewar Faransa: “‘Yan harigido ba su da hurumin alanta wannan bukata, amincewar jakadan ka iya fitowa ne daga halastattun hukumomin Nijar.