Layya Sunna ce maikarfi ga wanda ya sami iko mace ko namiji, ba wajibi bace sai dai idan mutum ne ya dorawa kansa, kamar ya yi alwashi cewa In ya samu wannan aikin ko in ya ci jarabawannan ko in medakin shi ta sauka lafiya sai ya yi layya, to da zarar abinda ya anbata ya auku layya ta zama wajibi akanshi.
Ko Mace Na Layyah?:
Amsa anan E ce domin duk abinda shari’ar musulunci ta zo da shi babu banbanci tsakanin mace da na miji sai abinda wani dalili na jinsi ya banbanta, saboda haka ya halatta mace ta yi layya kuma mijinta ya yi idan yana da hali hakanan ‘ya’ya maza da mata, mu sani layyah ba biki bace ibadace da ake baiwa mutum lada idan ya yi kamar yadda akace ya yi kuma ya yi shi domin Allah, anan yana dakyau maza su sani iyalansu ba gasa suke da su ba, ibadace da Allah Ya shar’anta ta akan maza da mata.
Ya Halatta Aci Bashi?: E, ya hallata ga mutumin da yake da tabbas na kudi ya ci bashi domin ya sayi dabbar da zai layya da ita, mu lura munce wanda yak e da tabbas, kamar ma’aikacin da yake jiran albashi, ko dankasun da ya sayo kaya ga shi jibge ba’a yana jiran masu saya.
Falalar Yin Layyah: Nana Aishah Allah ya kara mata yarda ta ruwaito cewa lallai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce ” Dan’adam bai taba yin wani aiki aranar Babbar Sallah ba da yafi soyiwa a gurin Allah kamar zubar da jinni ba. Lalle tabbas zata zo (tabbar layya) ranar kiyama da kahonta, da gashinta, kuma lallai jinin tabbas yana aukuwa ga Allah a wani wuri tun kafi ya diga a kasa, ku yi ta da dadin rai.” Tirmizi ya ruwato shi hadisi na 1493.