Daga Walid Hari.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin na shirin sanar da mamaye yankunan kasar Ukraine hudu – duk da gargadin Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa lamarin na iya ta’azzara yaƙi.
Fadar Kremlin ta Rasha ta ce za ta ayyana Kherson da Zaporizhzhia da Donetsk da Luhansk a matsayin yankinta a wani biki da za a gudanar a birnin Moscow.
Ukraine ta ce za ta ci gaba da yaƙin ‘yantar da yankunanta – duk da barazanar Mista Putin na amfani da duk makamin da yake da shi don kare yankunan.
Amurka da sauran kawayen Ukraine sun ce ba za su taba aminta da yankunan a matsayin Rasha ba.
Shugaba Biden ya ce matakin, keta haddin dokokin Majalisar Dinkin Duniya ne karara Rasha take yi, don haka gwamnatin birnin Washington za ta mayar da martani da sabbin takunkumai masu tsanani.