Sauke hakkin dake kanku shi zaisa gwamnati ta samu damar cigaba da ayyuka

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga Matakan gwamnatin su dunga yin amfani da kudaden shiga da suke samu ta hanyoyin da zasu cigaba ga kyautata rayuwar al’uma.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin taron kasa na shekara shekara da kungiyar Masana Tattalin arziki ta kasa wato “Nigerian Economic Society” ta shirya a dakin taro na jami’ar Maryam Abacha dake nan Kano a yankin karamar hukumar Tarauni.

Sarkin yayi kira ga al’uma su dunga biyan Kudaden da ya kamata su biya ga Gwamnati.

Yace hakan ne zai sa al’uma su cigaba da biyan kudaden shiga akan lokaci.

Sarkin ya bukaci Kungiyar su sami dangantaka da masu ruwa da tsaki akan sanin Tattalin arziki domin fadada ilimi da dabarun farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Yace jihar Kano jiha ce ta cibiyar kasuwanci bawai a arewacin kasar nan ba harma da kasashen duniya baki daya.

Alhaji Aminu Bayero yace tuntubar “Yan Kasuwa zai taimaka a samu wane bangare na ilimi wanda zai taimakawa bincike don samun nasarar farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace irin wannan tattaunawar tana da matukar muhimmanci a wajen al’umma kuma ta haka ne za’a cigaba da wayar da kan mutane hanyoyin da zasu runka biyan haraji.

Ya kuma yabawa shugabannin kingiyar busa kokarin da sukai wajan hada taron na kasa.

Da take nata jawabi, Shugabar kungiyar Farfesa Ummu Ahmad Jalingo tace sun shirya taron ne domin tattauna hanyoyin da za abi wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Tace hakan ne ma yasa suka yiwa taron na bana taken yadda za’a tabbatar da da’a wajen sarrafa kudade da hanyoyin manufofin Gwamnati wajen farfado da arzikin kasar nan.

Masana tattalin arziki daga sassan jami’oin kasar nan sun halarci taron na bana da Kungiyar ta gudanar anan jihar Kano.

Daga magatakardary labara  masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments