Cibiyar kolawda ta samu Damar kaima mai girma alhaji Aminu kabir ziyara bangirma da kummah sada zumunchi amatsayin shi na uba a cikin qungiyar
Wanan cibiya ta saba gudanar da ayyukan Alkhairi daban daban irin bada tallafi ga yara marayu da yan gudun hijira da marasa lafiya waanda ke kwance a asibiti kummah tana tallafama mata da kayan sanao,I da sauransu
A cewar shugaban cibiyar sun samu damar tattaunawa da mai girma Hakimin Mashi Alhaji Aminu Kabir, akan taron da zaayi na wanan qungiya a ranar 30 ga watan bakwai na wannan shekara abisa laakari da yanda iyayyen qungiyar suke kokari akan ita wanan qungiya.
shiyasa manbibin wanan qungiya suka ga ya kamata ace sun karrama wasu daga cikin iyayyen wanan qungiya
Kana sun yaba da da irin kyakkyawar tarba ta musamman daga baba uban kowa mai girma alhaji Aminu kabir kummah yaji dadi yayi farin ciki sosai da wanan ziyara