A yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023, ana ta karo da dirama a jam’iyyun siyasa daban-daban a Najeriya.
Cikin abubuwa masu daukar hankulan mutane akwai sakamakon zabukan fidda gwani, zargin bawa daliget toshiyar baki, musayyar maganganu da wasu abubuwan.
Sai dai guda daga cikin abin da mutane suka yawaita cece-kuce a kansa gabanin babban zaben 2023 shine batun takardun shaidar karatu.
A baya-bayan nan, wasu yan takarar sun gaza gabatar da satifiket dinsu inda suka bada uzuri na cewa sun bata ko kuma wasu dalilan.
Wasu manyan sunaye da wannan lamarin ta shafa sun hada da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na YPP, Abdulmalik Ado Ibrahim, dan takarar shugaban kasa na ADP, Sani Yabagi amma yanzu Takardar shaidar digiri (BSc) da NYSC na Peter Obi sun bayyana.
Kazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, shine dan takarar shugaban kasa na farko da ya fara bayyana satifiket din digiri dinsa da na yi wa kasa hidima wato NYSC.