Babbar Jam’iyar adawa a Nageriya ta PDP ta bada Sanarwar dakatar da wasu jigajigan jam’iyar guda biyu.
Dakatarwar ta taso ne tun daga tushe inda aka dakatar da Senato George Thompson Sekibo daga mazabar sa dake karamar hukumar Boko
Sai kuma mai biyeasa baya ritaya Hon. Dacta Austin Adele na karamar hukumar birnin Fatakwal
Sai dai a nasa bangare kwamitin kolin jam’iyar ya yi watsi da wancan ikrari na shugabannin mazabar inda yace duba da gudunmawar da suke bayarwa basu chanchanci wannan hukuncin ba