Da misalin karfe 4 na yamma agogon GMT, lokacin da ya kamata yarjejeniyar da aka ce an cimma din ta fara aiki, ana iya jiyo karar harbe-harbe a kafatanin birnin Khartoum.
Mutane suna ta tsere wa dag khartoum babban birnin Sudan bayan kwana hudu da fara yakin / Hoto: AFP
An ci gaba da jin karar fashewar abubuwa a Khartoum babban birnin Sudan, kwana hudu da fara yakin da ya hallaka kusan mutum 200, duk da ikirarin tsagaita wuta da aka ce an yi.
Bayan shiga tsakanin da kasashen duniya suka yi, Kwamandan Rundunar Rapid Support Forces [RSF], Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemetti, ya ce zai amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa’a 24 a ranar Talata, wanda rundunar sojin kasar ta ce ba ta da wata masaniya a kai, kafin daga baya kuma ta zargi RSF da karya ta.
Tuni Rundunar RSF ta soki gwamnatin da karya yarjejeniyar.
Da misalin karfe 4 na yamma agogon GMT, lokacin da ya kamata yarjejeniyar da aka ce an cimma din ta fara aiki, ana iya jiyo karar harbe-harbe a kafatanin birnin Khartoum, kamar yadda shaidu da yawa suka fada, kuma an ci gaba da jin hakan har zuwa dare.
“Har zuwa yanzu ana ci gaba da yakin a Sudan, ciki har da birnin Khartoum da sauran wurare. Babu alamar kawo karshen fadan,” a cewar mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Dagalo ya sanar da batun yarjejeniyar ce bayan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya yi magana da janar-janar din biyu inda “ya nemi a yi gaggawar tsagaita wuta.”
Ministocin Harkokin Wajen Kasashe Bakwai Masu Karfin Tattalin Arziki na G7, wadanda suka hada da Amurka, su ma a ranar Talata sun yi kira ga bangarorin biyu masu fada da juna da su yi gaggawar dakatar da yakin, a yayin da ake jin kararrakin fashewar abubuwa a Khartoum, inda mayakan sa kai masu rawani ke ta sintiri a kan titunan birnin.
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, kan hanyoyin da za a bi a dakatar da fadan tare da kwantar da hankula a Sudan.
Amurka ta ce an bude wa wata tawagar jami’an diflomasiyyarta wuta sannan kuma an kai wa jakadan Kungiyar Tarayyar Turai hari a gidansa.
Kungiyoyin bayar da agaji sun ce ana ta satar kayayyakin kula da lafiya da sauran kayan agaji.
Akwai fargabar cewa rikicin ka iya bazuwa zuwa sauran sassan kasar ta hanyar kai hare-haren sama.
Ganau sun ce an girke manyan motoci masu dauke da bindiogin kakkabo jiragen sama a unguwannin mutane a Khartoum tun da safiyar ranar Talata.
An farfasa gilasai da tagogi na gidajen mutane da ofisoshi da dama a fadin birnin