Mallam Nuhu Ribadu, mataimakin babban sufeton ‘yan sanda (mai ritaya) a hukumance ya karɓi aikin Mashawarcin Tsaron Ƙasa a Najeriya daga Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
Yayin wata ganawa ranar Litinin a Abuja, Ribadu bayan kama aiki, ya yi alƙawarin zage damtse don cika burin da ‘yan Najeriya ke da shi da kuma tabbatar da tsaron ƙasar daga duk wani nau’in rashin tsaro kama daga ayyukan ta’addanci da ‘yan fashin daji da satar mutane don neman kuɗin fansa da sauransu.
“Za mu daidaita al’amuran ƙasar nan, za mu tabbatar da tsare ƙasar nan kuma mu tabbatar da zaman lafiya a Najeriya saboda mun yi imani lokaci ya zo da ƙasar nan za ta ci moriyar zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankali da zaman doka kamar dai kowacce ƙasa a duniya,” Ribadu ya ce a cikin jawabinsa.
“Tsaron ƙasa, al’amari ne da ake ci gaba da ginawa. Za mu yi nazari a kan ƙoƙarin da aka rigaya aka yi kuma mu ɗora a kai.
“Shugaban ƙasa ya ɗauki babban nauyi na tabbatar da tsaron duk wani taku na ƙasar mu. Za mu yi aiki da duk wani mai ruwa da tsaki don tabbatar da ganin an cika wannan buri.
“Wannan gagarumin aiki na tabbatar da tsaron ƙasarmu, nauyi ne a kan duk ɗan Najeriya da ma dukkan abokan ƙawancen Najeriya,” ya faɗa a cikin wata sanarwa daga ofishin Mashawarcin tsaron ƙasar.
Tun da farko an naɗa Ribadu, wanda shi ne shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na farko a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Sai dai bayan ‘yan kwanaki, sai Shugaba Bola Tinubu ya yi wa dukkan manyan hafsoshin tsaron ƙasar murabus tare da naɗa wasu a gurabensu ciki har da Mallam Nuhu Ribadu wanda aka ɗaga darajarsa zuwa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro