Wasu masu gine-gine a jihar Kano na ci gaba da bayyana halin zaman Dar-dar da suke ciki da fargaba, sakamakon yiwuwar rushe musu gini daga nan zuwa kowanne lokaci.
Masu irn wadannan gidaje sun ce tuni an shafa masu jan fentin gargadi, wata alama da ke nuna cewa daga nan zuwa kowanne lokaci za a iya zuwa a rushe musu gidajen nasu.
Wani magidanci a unguwar Salanta ya bukaci gwamnatin ta duba wannan al’amari duba da halin da suka tsinci kansu.
A cewarsa ”Ni ba dan siyasa ba ne, kuma ‘yan unguwar nan gwamnati suka zaba, an bi mu kasuwa yanzu an biyo mu gida za a hana mu barci, ya kamata a duba wannan al’amari, mun bi ka’ida amma ana son a fitar da mu daga gidajenmu”.
Alhaji Abubakar Zakari Muhammad wani da ya garzaya kotu don kalubalantar shirin rushe gidansa bayan an shafa masa jan fenti, ya ce yanzu haka magana na gaban kotu, kuma tuni an ba wa hukumar tsara birane ta jihar umarnin dakatawa har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci.
Suma a nasu bangaren ƴan kasuwa da lamarin ya shafa na ci gaba da kokawa kan irin asarar da rusau ɗin ya janyo musu.
Alhaji Sharif Nata’ala Isma’il, shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin ƴan kasuwa na kasuwar Kofar Wambai, kuma ya shaida wa BBC cewa sun yi asarar da ta kai ta Naira Biliyan guda.
”Yanzu haka a kasuwa muke kwana, don kowanne lokaci za a iya shigowa a mana abun da ba shi kenan ba, a razane muke, a matsayin gwamnati na uwa ya kamata ta tausaya mana” in ji shi.