Hukumar yaki da masu yin Almundahna da AYYUKA masu alaka cin hanci da rashawa ta ICPC ta kama karin sabbin kudin da babban bankin kasarnan ya bukaci a rarraba su ga alumma kimanin Naira miliyan 258 a wani Banki dake Abuja
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar ICPC, Azuka Ogugua, shine ya bayyana hakan ga manema labarai
Ya hukumar ta gudanar da rangadi ne biyo Bayan zargin bankunan yan kasuwa sun yi kunnen uwar shegu da umarnin babban bankin kasa wato CBN.
Ya kara da cewa tun kafin aiwatar da samamen sun Sami bayani akan bankin ya tare kudaden kuma ya ki rabawa ressan sa dake fadin kasar nan hakan ce ta basu damar kai samamen har suka kama tarin kudaden.
Kazalika ya ce million biyar biyar kawai bankin ya aike wa wasu ressan sa a cikin kudaden da ya karba daga apex bank
Amma tuni aka kama jagororin Bankin duk da cewa an damka su a hanun belli kuma za’a ci gaba da bincike